Posts

TABIZARO

TABIZARO Akwai matan aure da yawa a wannan lokacin da ke daukar cewa ballagazanci da rashin suturta jiki ko rashin kamun kai wani abu ne na burgewa ko kuma wayewa. Sau tari za ki ga matar aure ta tare keke bayan tana ganin kartin maza har biyu a ciki ta shige ta zama ita ce cikon ta uku. Ga mata kuma ba su iya zaman abin hawa ba. Wa su da gangan ma su ke jingina jikinsu a jikin namijin da ba muharramin su ba. Wannan ba karamin abu ba ne musamman ma a addini da kuma al'adunmu. Amma saboda an cire kunya ta ya macen malam bahaushe daga zukatan mu sai ku ga mata ko damuwa da wannan kwamacalar ma ba sun daina yi  Addini ya hana muharramai su zauna daf da daf da juna ta yanda har dayan zai dinga jin kamshin dayan saboda gudun kada Iblis ya zama ya shiga tsakaninsu ya kuma kimsa musu miyagun tunanin da zai iya kaiwa ga aikata lalata ko kuma kusantar ta. Allah cewa ya yi kada a kusanci Zina saboda haka duk wani abu da zai iya kusanta mutune zuwa gare ta ma riga an kawo shamaki da shinge an...

ILLAR YIM OLANNING GA AMARYAR DA BATA TAƁA HAIHUWA BA

ILLAR YIN PLANNING GA AMARYAR DA BATA TABA HAIHUWA BA kasancewar an sha shagulgulan bukuwa a karshen shekarar nan kuma ana kan shirin yin wasu daga nan har zuwa Watan Sallar Tsofaffi mu ka ga dacewar yin wannan fadakarwa kan kasadar da wasu angwaye da amare su ke yi na yanke danyen hukumcin fara yin dabarun planning tun kafin aje ga daukar cikin farko. Kowane iyali da irin ragon dalilin da su ke bayarwa na aikata wannan kasassaba daga ciki ga wasu mun kawo a kasa: 1. Samun Damar Cin Amarci Wasu da yawa kan fake da cewa daukar ciki daga yin aure kan hana su yin rawar gaban hantsi yanda su ke so.  Saboda haka sai su fara anfani da dabarun bada tazarar haihuwa cikin rashin sanin abinda hakan kan iya haifarwa a rayuwar auren su ta nan gaba. 2. Gudun Suratai da Zargi Wasu kuma su na anfani da dabarun bada tazara ne wai don kada a dinga cewa sun haihu da wuri. Akwai mata masu kafirin surutu da za ku ji suna fadar kalmomi kamar cewa: "kamar a dokin kofa da dauki cikin."  Wasu ...

ZINAR MA'AURATA A WANNAN ZAMANIN INA MAFITA?

Shin ko wadanne dalilai ne ke sanya ma'aurata aikata zina a wannan lokacin?  A zamanin baya mazaje aka fi sani da wannan kazamar ta'ada amma anzu ana yawan samun korafe-jorafe kan cewa matan aure wai suna alaka da wasu maxajen na daban.  A watannin baya a jihar Kano an sami wata mata da ta hallaka mijinta wanda makotan su su ka tabbatar da cewa dalilin hakan ya afku ne bayam da ya gano ta na aikata haramtacciyar alaka da wani kwartonta  Babban abinda mu ke son sani shi ne meye ma ya ke janyo wannan ? Daga bisani kuma mu lalubo bakim zare wajen sanan ina mafita domim yiwa tufkar hanci. A zamanin da an tabbatar da cewa matar bahaushe ba ta cin amanar aure.  Amma to me ya sa rana tdaka kwatsam ake aamun irin wadannan miyagun labaru.  A namu nazarin dai akwai tasirin shafukan holewa da kawance na yanar gizo-gizo wadanda ke hada mummunar alakar da ke janyo wannan matsala.

SOYAYYA BATA RIƘE AURE

Image
SOYAYYA BA TA RIKE AURE Ko kun san me ya sa ango da amarya ke samun sabani jimm kadan bayan an shiga daga ciki? Babban dalilin shi ne cewa aure ba ya rikuwa da iya soyayya kadai. Eh abinda na fada hakan ku ka ji. Soyayya bata rike aure. Wannan batu 'mujarrabun' ne inji masu bada lakani. Za ku ga ma'aurata masu kaunar juna kamar daya ya hadiye dayan saboda tsabagen bege da yanda su ke son juna, amma da zarar an dan kwana biyu da shiga dakin aure wani ma har zage kwanji ya ke ya shirga mata dan karen duka. Wata kuma ko tsiwa da caccaba maganar da mitar amaryar ma ba sa iya barinsa ya komo gida sai ya tabbatar cewa ya na shigowa sai kwanciya barci. Dalilin da ke janyo haka kuwa shi ne cewa shi aure rayuwa ce ake son yi ta dindindin yayinda shi kuma neman aure da lovanyar waje duk flashing ne da kamfen irin na yan siyasa kafin zabe, to a daidai lokacin da kowa ya fahimci zahirin gaskiyar yanda ta ke sai ku ji an fara samun hatsaniya da korafe-korafe. Mafita  daya ce kowa ya dau...

AURE-JAHANNAMA KO ALJANNAR DUNIYA?

Aure Aljannar Duniya ne ko Jahannamar Duniya Gidan aure kan iya zama wata aljannar duniya ko kuma karamar Jahannamar duniya. Yanda duk abin zai kasance wani zabi ne da ke hannun maauratan a mafiya yawan lokuta. Fahimtar juna ita ce mafi mahimmancin dalilan da su ka sanya ake yin tadi ko zance tsakanin saurayi da budurwa masu shirin zama miji da mata a kasar Hausa. Amma a halin yanzu mun fi mayar da hankali ne kan labarun abubuwan da ake yayi a kafafen sada zumunta ko hirar kwallo idan saurayin mayen ball ne ko kuma ma a fara wuce gona da iri wajen fara shasshafa juna. Ana barin kari ne tun ran tubani ko kuma barin zane tun rana da aka gina tukunya. Idan ba'a dauki hanyar fahimtar juna da sanin mabanbantan halayen juna a mabanbantan lokuta ba, to fa tabbasa zaman aure ya kan zamo mai matukar wahala kamar dai kangin bauta. Amma idan Allah ya sa aka fahimci juna to daman ance idan ka san halin mutum sai ka ci maganin zama da shi sai a ga zama ya samu lafiya lumai. Duk da cewa dai wasu...

HIRAR TOFON RAI

Image
HIRAR TOFON RAI ko kun san amfanin zama a dinga tattaunawa da iyali kuwa?  Shin bayan duk kulawa da mu'amalar aure da aka sani kuna iya ware lokaci na.musamman domin tattaunawa da warware matsalolin cikin raha da nishadi?  Ko kum san cewa idan matsalolin aure idan su ka taru kuma ba'a bada damar zama a tattauna zama su ke yi kamar wata nakiya mai wanin agigon fashewa?  Shi kun san da cewa zama a tattauma tsakanin masoyan ma'aurata ya na ƙara tsawon rai kuwa? Hausawa sun daɗe da gano wannan tun ma kafin binciken kimiyya ya tabbatar da hakan. Wannan ya sa Hausawa ke kiran irin wannan hirar da sunan: 'Hirar Tofon Rai!' Allah ya ƙara danƙon ƙauna ya tarwatsa aniyar iyalan Iblis masu son tarwatsa sunnar Mustapha ta hanyar manafunci da kinibibin shigaɓtsakamin masoyan ma'aurata ta hanyar kawo musu matsalolin da suɓke ƙara taɓarɓara lamura!

HUTSUN MIJI DA MACE MAI TSIWA

HUTSUN MIJI DA MACE MAI TSIWA Babban abinda ya sa ake cewa Allah ya saɓa halaye a lokacin da aka ɗaura aure shi ne gudun irin wannan haɗin bautar tsakanin hutsun miji da miskilar mace ko kuma mai tsiwa. Idan tsautsayi ya sa aka yinrashin sa'a hakan ta faru kuma har aka je abin ya kai ga aure to fa sai a fara jan wuridin LA HAULA WALA QUWWATA.......