HIRAR TOFON RAI

HIRAR TOFON RAI

ko kun san amfanin zama a dinga tattaunawa da iyali kuwa? 

Shin bayan duk kulawa da mu'amalar aure da aka sani kuna iya ware lokaci na.musamman domin tattaunawa da warware matsalolin cikin raha da nishadi? 

Ko kum san cewa idan matsalolin aure idan su ka taru kuma ba'a bada damar zama a tattauna zama su ke yi kamar wata nakiya mai wanin agigon fashewa? 

Shi kun san da cewa zama a tattauma tsakanin masoyan ma'aurata ya na ƙara tsawon rai kuwa?

Hausawa sun daɗe da gano wannan tun ma kafin binciken kimiyya ya tabbatar da hakan.

Wannan ya sa Hausawa ke kiran irin wannan hirar da sunan: 'Hirar Tofon Rai!'

Allah ya ƙara danƙon ƙauna ya tarwatsa aniyar iyalan Iblis masu son tarwatsa sunnar Mustapha ta hanyar manafunci da kinibibin shigaɓtsakamin masoyan ma'aurata ta hanyar kawo musu matsalolin da suɓke ƙara taɓarɓara lamura!

Comments

Popular posts from this blog

SOYAYYA BATA RIƘE AURE

HUTSUN MIJI DA MACE MAI TSIWA

GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA