SOYAYYA BATA RIƘE AURE

SOYAYYA BA TA RIKE AURE

Ko kun san me ya sa ango da amarya ke samun sabani jimm kadan bayan an shiga daga ciki? Babban dalilin shi ne cewa aure ba ya rikuwa da iya soyayya kadai. Eh abinda na fada hakan ku ka ji. Soyayya bata rike aure. Wannan batu 'mujarrabun' ne inji masu bada lakani.

Za ku ga ma'aurata masu kaunar juna kamar daya ya hadiye dayan saboda tsabagen bege da yanda su ke son juna, amma da zarar an dan kwana biyu da shiga dakin aure wani ma har zage kwanji ya ke ya shirga mata dan karen duka. Wata kuma ko tsiwa da caccaba maganar da mitar amaryar ma ba sa iya barinsa ya komo gida sai ya tabbatar cewa ya na shigowa sai kwanciya barci.

Dalilin da ke janyo haka kuwa shi ne cewa shi aure rayuwa ce ake son yi ta dindindin yayinda shi kuma neman aure da lovanyar waje duk flashing ne da kamfen irin na yan siyasa kafin zabe, to a daidai lokacin da kowa ya fahimci zahirin gaskiyar yanda ta ke sai ku ji an fara samun hatsaniya da korafe-korafe.

Mafita  daya ce kowa ya dauki abokin aurensa a matsayin amini. Idan mu ka lura da yanda  aminai su ke, su kan yi shekaru saba'in ko sama, tun lokacin su na da jajayen sahu har lokacin da su ka takwarkwashe amma ku ji cewa ba'a taba jin kan su. Dole ne sai abokan zaman aure sun amince da cewa su aminan juna ne da ke nuna soyayya, kulawa,  tarairaya, tausayin juna, sannan uba da juriya (tolerence) wadannan abubuwa su ne aka tabbatar su ne sanya aminai zama tsawon shekaru ba tare da an ji kan su ba ko sau daya. Duk abinda ya faru tsakanin su su ke kashewa su binni.

Abinda magabata ke nufi da ayi HAKURI kenan a duk lokacin da su ke yi wa sabon ango da sabuwar amarya nasiha kafin a mika su zuwa gidan su. A harshen mu na Hausa ba mu da wata kalmar da ta ke kusa da tolerance sai dai hakuri. Wannan ne ma yasa wasu amaren yan bana bakwai su ke cewa: su ba wai zaman hakuri za su yi ba a gidan aure tunda wai auren soyayya su ka yi, saboda sam ba su san dawan garin ba.

Dole ne bayan yin auren soyayya sai an koyi iya zama da juna da yi wa juna uzuri da iya sauraren juna sannan fa wannan zaman zai dore.

Shekarun baya Ghali DZ ya taba yin wata waka wadda a halin yanzu na daina jin ana sanya ta ko a gidajen rediyo, wadda a cikin wakar ya ke sukar lamirin zaman hakuri a gidan aure da ake yawan fada a kasar Hausa.

Ga amshin wakar Ghali DZ din ko wani ya na da ita ya turo mana ta inbox:

"Wai-wai-wai, wai-wai nima na ke ji
Wai idan an yo aure,
Soyayya ta kare sai zaman hakuri....?"

Comments

Popular posts from this blog

HUTSUN MIJI DA MACE MAI TSIWA

GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA

MATSALAR SHAYE-SHAYE