GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA
GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA
Shin ku na cikin magidanta da su ke cacar baki a gaban yaran su? Idan ku na cikin masu yin hakan to akwai gagurmar matsala da saƙon da ku ke isarwa zuwa gare su.
Yawanci dai bincike ya nuna cewa duk ma'auratan da su ke irin wannan halayyar to su ma Idan aka tsawaita bincike tasowa su ka yi su ka ga na su iyayen su na aikata irin wannan mummunan halin.
Kun ga kenan hanya ɗaya da za'a iya takawa wannan abu burki shi ne ta dakatar da abin daga kan ku kafi ku cigaba da shuka shi ya na ƙara tofon girma da yaɗo a zukatan ƴaƴan ku inda su ma za su aikata hakan ga ƴaƴan wasu a nan gaba.
Babu wata matsalar da tattaunawa ba za ta iya magance ta ba.
Comments
Post a Comment