AURE HALAL
WAKAR AURE HALAL Farko da Allah da yacce kar mu doshi zina Muiwo rikon aure mu zauna babu ishkali Bayan salati da taslimi gunsa Sayyidina Mata sahabbai kasa harma dukan ali Sai godiya gun sa Allah wanda bai da kini Horewa dukkan mu don aure mu san hali Aure fa sunna ce da mai kyamarta bai zama ba Face cikin wanda bai da rabo a tun azali Na so ace na tara ilmai fannuka dayawa Da na zubo su akan auren ya zam fili Amma karambani nake so zanyi don nagwada Allah ka min tanyo ya zamto babu ishkali Tun sanda Allah yai Adam aure ya zam hanya Ya sanya aure ya zam hanya ta ifsali Gadon mu ne aure gama domin da shi mu ka zo Duk wanda yayyi musu to bai da kyan asali Komai na aure ba na yarwa danbuwa ka sani Lada na aure fa na nan mai yawansa tuli Aure cikinsa akwai kauna da jinkai ma Ga dukkanin jinsukan nan har zuwa ajali Aure ka sa nutsuwa aure ka sa haske Kai harda annashuwa goshi ya zam kyalli Kai duk abin ma da zance ba ku gane ni Kai dai kaje ka bido indai akwai hali ...