AURE HALAL
WAKAR AURE HALAL
Farko da Allah da yacce kar mu doshi zina
Muiwo rikon aure mu zauna babu ishkali
Bayan salati da taslimi gunsa Sayyidina
Mata sahabbai kasa harma dukan ali
Sai godiya gun sa Allah wanda bai da kini
Horewa dukkan mu don aure mu san hali
Aure fa sunna ce da mai kyamarta bai zama ba
Face cikin wanda bai da rabo a tun azali
Na so ace na tara ilmai fannuka dayawa
Da na zubo su akan auren ya zam fili
Amma karambani nake so zanyi don nagwada
Allah ka min tanyo ya zamto babu ishkali
Tun sanda Allah yai Adam aure ya zam hanya
Ya sanya aure ya zam hanya ta ifsali
Gadon mu ne aure gama domin da shi mu ka zo
Duk wanda yayyi musu to bai da kyan asali
Komai na aure ba na yarwa danbuwa ka sani
Lada na aure fa na nan mai yawansa tuli
Aure cikinsa akwai kauna da jinkai ma
Ga dukkanin jinsukan nan har zuwa ajali
Aure ka sa nutsuwa aure ka sa haske
Kai harda annashuwa goshi ya zam kyalli
Kai duk abin ma da zance ba ku gane ni
Kai dai kaje ka bido indai akwai hali
Aure sila ce ta samun arzikin dunya
Dukkan ciyarwar da kai na nan a kan kaili
In saduwa ku ka yi ladan ta na dayawa
Kai nayi al'ajabi lada cikin shagali
Tun lokaci na sahabbai sunyi mamaki
Domin akwai zunubi indai akai badali
Yayin da Allah ya koro kan batun aure
Ya ratsa sallah ta wusda mun ga tafsili
Wannan ka nuna batun aure azimun ne
Don kar mu yo wasa mu fada can cikin zilli
Mata ta aure ku san ai ta wuce Huri
Don tai ibada ta taklifi nan cikin fili.
Gwauro, tuzuru kaza zawari da ma zawara
Aure ku yo don gudun tono na silili
Comments
Post a Comment