MATSALOLIN DA KE ADDABAR AURE A KASAR HAUSA
Mata kan ce wai aure raine da shi. Amma alamu na nuna cewa tsahon ran auren iyayen mu da kakanninmu ya fi na mu tsaho nesa ba kusa ba. Tunda ana samun auren da ya zarta shekara sittin a da, amma yanzu har auren kwana uku an samu a kasar Hausa. Wannan babban dalilin da ya sa wasu kabilun da su ke kallon Bahaushe da ga nesa su ke hana su auren yayansu.
A kasa mun sake kawo wasu jerin dalilan da su kan kawo mutuwar aure cikin kankanin lokaci kamar yanda muka taba kawowa a wani rubutu da muka walƙafa a baya.
1) Rashin tsoron Allah
2) Rashin daukar aure a matsayin ibada
3) Karya kafin aure
4) Matsalar jahiltar auren ma kansa
5) Matsalolin rashin gyaran turaka
6) Matsalar rashin iya girki
7) Matsalar shaye-shaye
8) Matsalar tattalin arziki
10) Matsalar surukai (iyayen ma'aurata)
11) Matsalar abokiyar zama
12) Matsalar facala
13) Matsalar dangin miji ko mata
14) Matsalar zaman gidan haya
15) Matsalar makota
16) Matsalar miyagun abokai da kawaye
17) Matsalar cutuka
18) Matsalar cin amanar juna (lalata)
19) Matsalar cin amanar juna (maɗigo da neman maza)
20) Matsalar rashin haihuwa
Matsalar leke
21) Matsalar dukan mata
22) Matsalar kazanta
23) Matsalar kazanta
24) Makircin bokaye wajen raba aure
25) Matsalolin wayar hannu da kafofin sadarwar yanar gizo
Kadan kenan da ga matsalolin da hankalin mu ya kai kai a halin yanzu. Muna fatan zamu dinga daukansu daya baya muna yin bayani akai da yanda za'a shawo kan su cikin yardar Allah.
Mu na kira ga mabiyan mu da idan sun hangi wata matsalar da ba mu kawo ba za su taimaka su sanyata a sashen sharhi wato comment.
Mu na kara godiya kwarai da gaske masoya da mabiya wannan shafi mai albarka.
Comments
Post a Comment