ZINAR MA'AURATA A WANNAN ZAMANIN INA MAFITA?
Shin ko wadanne dalilai ne ke sanya ma'aurata aikata zina a wannan lokacin? A zamanin baya mazaje aka fi sani da wannan kazamar ta'ada amma anzu ana yawan samun korafe-jorafe kan cewa matan aure wai suna alaka da wasu maxajen na daban.
A watannin baya a jihar Kano an sami wata mata da ta hallaka mijinta wanda makotan su su ka tabbatar da cewa dalilin hakan ya afku ne bayam da ya gano ta na aikata haramtacciyar alaka da wani kwartonta
Babban abinda mu ke son sani shi ne meye ma ya ke janyo wannan ? Daga bisani kuma mu lalubo bakim zare wajen sanan ina mafita domim yiwa tufkar hanci.
A zamanin da an tabbatar da cewa matar bahaushe ba ta cin amanar aure. Amma to me ya sa rana tdaka kwatsam ake aamun irin wadannan miyagun labaru.
A namu nazarin dai akwai tasirin shafukan holewa da kawance na yanar gizo-gizo wadanda ke hada mummunar alakar da ke janyo wannan matsala.
Comments
Post a Comment