TABIZARO
TABIZARO
Akwai matan aure da yawa a wannan lokacin da ke daukar cewa ballagazanci da rashin suturta jiki ko rashin kamun kai wani abu ne na burgewa ko kuma wayewa. Sau tari za ki ga matar aure ta tare keke bayan tana ganin kartin maza har biyu a ciki ta shige ta zama ita ce cikon ta uku. Ga mata kuma ba su iya zaman abin hawa ba. Wa su da gangan ma su ke jingina jikinsu a jikin namijin da ba muharramin su ba.
Wannan ba karamin abu ba ne musamman ma a addini da kuma al'adunmu. Amma saboda an cire kunya ta ya macen malam bahaushe daga zukatan mu sai ku ga mata ko damuwa da wannan kwamacalar ma ba sun daina yi
Addini ya hana muharramai su zauna daf da daf da juna ta yanda har dayan zai dinga jin kamshin dayan saboda gudun kada Iblis ya zama ya shiga tsakaninsu ya kuma kimsa musu miyagun tunanin da zai iya kaiwa ga aikata lalata ko kuma kusantar ta.
Allah cewa ya yi kada a kusanci Zina saboda haka duk wani abu da zai iya kusanta mutune zuwa gare ta ma riga an kawo shamaki da shinge an tokare shi.
Comments
Post a Comment