AURE-JAHANNAMA KO ALJANNAR DUNIYA?

Aure Aljannar Duniya ne ko Jahannamar Duniya

Gidan aure kan iya zama wata aljannar duniya ko kuma karamar Jahannamar duniya. Yanda duk abin zai kasance wani zabi ne da ke hannun maauratan a mafiya yawan lokuta.

Fahimtar juna ita ce mafi mahimmancin dalilan da su ka sanya ake yin tadi ko zance tsakanin saurayi da budurwa masu shirin zama miji da mata a kasar Hausa. Amma a halin yanzu mun fi mayar da hankali ne kan labarun abubuwan da ake yayi a kafafen sada zumunta ko hirar kwallo idan saurayin mayen ball ne ko kuma ma a fara wuce gona da iri wajen fara shasshafa juna.

Ana barin kari ne tun ran tubani ko kuma barin zane tun rana da aka gina tukunya. Idan ba'a dauki hanyar fahimtar juna da sanin mabanbantan halayen juna a mabanbantan lokuta ba, to fa tabbasa zaman aure ya kan zamo mai matukar wahala kamar dai kangin bauta. Amma idan Allah ya sa aka fahimci juna to daman ance idan ka san halin mutum sai ka ci maganin zama da shi sai a ga zama ya samu lafiya lumai.

Duk da cewa dai wasu halayen sam ba sa bayyana sai bayan an shiga daga ciki, amma dai akalla za'a fahimci wasu masu tarin yawa idan da ace ana tsayawa ana yin tadin kamar dai yanda al'ada ta tanda da kuma bibiyar dalillan yin sa.

Lambun Ma'aurata

Comments

Popular posts from this blog

SOYAYYA BATA RIƘE AURE

HUTSUN MIJI DA MACE MAI TSIWA

GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA