ILLAR YIM OLANNING GA AMARYAR DA BATA TAƁA HAIHUWA BA

ILLAR YIN PLANNING GA AMARYAR DA BATA TABA HAIHUWA BA

kasancewar an sha shagulgulan bukuwa a karshen shekarar nan kuma ana kan shirin yin wasu daga nan har zuwa Watan Sallar Tsofaffi mu ka ga dacewar yin wannan fadakarwa kan kasadar da wasu angwaye da amare su ke yi na yanke danyen hukumcin fara yin dabarun planning tun kafin aje ga daukar cikin farko.

Kowane iyali da irin ragon dalilin da su ke bayarwa na aikata wannan kasassaba daga ciki ga wasu mun kawo a kasa:

1. Samun Damar Cin Amarci

Wasu da yawa kan fake da cewa daukar ciki daga yin aure kan hana su yin rawar gaban hantsi yanda su ke so.  Saboda haka sai su fara anfani da dabarun bada tazarar haihuwa cikin rashin sanin abinda hakan kan iya haifarwa a rayuwar auren su ta nan gaba.

2. Gudun Suratai da Zargi

Wasu kuma su na anfani da dabarun bada tazara ne wai don kada a dinga cewa sun haihu da wuri. Akwai mata masu kafirin surutu da za ku ji suna fadar kalmomi kamar cewa: "kamar a dokin kofa da dauki cikin."  Wasu kuwa har wasu maganganu za ku jinsu na yi na neman sheganta dan da aka haifa ganin cewa watanni bakwai an juye jariri.  To wannan yakan sanya wasu su fara anfani da wadannan sinadaran ba tare da sanin cewa kasada ce su ke dauka ba.

3 Ganin Kamun Ludayin Ango

Akwai wasu matan kuma da suke aikata wannan ba tare ma da sanin angon ba da zumma cewa wai idan zama yayi dadi za su cigaba sa zama idan kuma  sun fahimci cewa mijin nan ba zai yi dadin zama ba bisa abinda su ka fahimta na dan zaman da su ka yi da shi to sai su nemi rabuwa tunda daman ba haihuwa da shiga tsakanin su. A irin wannan tabargazar akwai matar da na sani jami'ar lafiya ce kuma duk yayanta mata sai ta dankara musu allurar watanni saboda wai gudun kada a sanya yayanta cikin kangin da haihuwa da kulafucin yaya za su hana su raba auren.  Kun ji fa mugun nufi da mummunan tunani.

4 Fakewa da Karatu

Wasu kuma suna dankarar sinadaran hana daukar juna biyu ne wai saboda kada da shigar ta ta sami cikin da zai iya zuwa da laulayi wanda hakan kan iya shafar karatun da ta riga ta fara.  Sai a yi ta dankarar kwayoyi ko allura da zummar cewa har sai an ga karshen biron boko sannan a dawo kan batun samun yaya.

5 Tsoron Talauci

Wannan shawarar tsiyar da hutsubar shedan kuma ta fi zuwa daga mijin da yawanci yana da wata matar sa ta fari ko matan sa ma wadansa tuni sun haifa masa yaya ya bar iri saboda hakan ne ma ya ke ganin shi ba shi da wata asara idan ya jefa sabuwar amaryar sa cikin garari da barazanar zama juya tun kafin ita ma ta ga irin na ta kwan.  Duk amaryar kuwa da ta amince da mijinta wajen fara dankarar sinadaran hana daukar ciki saboda wancan ragon uzurin nasa to duk abinda ya same ta daga baya ta sani cewa ita ce ta janyowa kanta.

Illolin yin hakan

Yawanci indai ma'aurata asibin gwamnati su ka je neman shawara sai an sanar da su cewa ba'a fara baiwa wadda bata taba haihuwa ba sinadaran planning saboda gudun matsaloli. Wasu daga cikin matsalolin kuwa sun hada da:

Daukewar al'ada gaba daya wadda za ta jefa yarinya karama zuwa ga expire tun ba ta taba ganin danta na cikinta ba.  Wanna kuwa ya fi faruwa ne kan amaren da daman sun dan kwana biyu a gida ba su sami shiga daga ciki ba.

Abinda ya ke faruwa kuwa shi ne: kwakwalwar su dai ta riga ta tabbatar cewa sun fara jinin al'ada tun su na firamare ko kuma karamar makarantar gaba da firamare, to duk lokacin da aka fara anfani da wadannan sinadaran sai kwakwalwar ta birkice kuma ta dauka cewa har tsufa ya cin musu sun shiga lokacin menopause wato lokacin zama juya ta hanyar daukewar jinin al'ada kwata-kwata da kuma kandashewar gaba da tankwarewar duk wani abu da ke iya jan hankalin da namiji dake jikinta (daman an halicce su ne saboda jan hankalin maza domin ya kai ga saduwa don a samun yaya duk mun san wannan adaptation din a biology ).

Masala ta biyu kuwa ita ce barkewar jini da kuma al'ada mai wasa (zuwa da daukewa akai-akai)  Kasancewar amarya bata taba haihuwa ba balle har ta yi shayarwa,  to sinadaran bada tazara kan rikita mata kwakwalwa ta dinga zubar jiji ba iyaka ko kuma rikicewar al'adar da za ta iya hana ta sakat ta bangaren ibada da kuma rayuwar auren kan ta.

Mafita

Ya kamata ma'aurata su fara bari su yi haihuwa ko daya ce tukuna kafin fara tunanin shiga tsarin bada tazara domin gudun taka san barawo.  Wata matar daman can Allah ya rubuta cewa ba za ta taba haihuwa ba.  Kun ga daga yin bada tazara na wani dan lokaci sai kawai aga abin ya zarce daga baya kuma azo ana zance da karkata kai da kuma zargin juna da cewa: kai ne ka jawo min shi kuma ango ya ce ai ke ki ka ce ayi hakan.

Hakazalika masana fannin lafiyar iyali na tsanantawa akan shawarar cewa a dakata da duk wani tsarin bada tazara da ake anfani da shi matukar anyi shekaru hudu (4) cif a jere ana gudanar da shi, domin kuwa shi kan sa bature bai yi sinadaran nan ba don ayi ta bankar su har abada.  An yi su ne domin bada tazara kamar yanda sunan su ya nuna.  Duk kuma mijin da ya dage cewa sai kin cigaba da anfani da planning bayan shekaru hudu (4) a jere to wallahi ya tasamma hanyar illata ki da nakasa miki mahaifar ne ma baki daya.  Dayawa daga cikin ku shaidu ne kan irin wannan matsalar da take faruwa kan matan da su ka dauki lokaci mai tsayi suna planning a karshe kuma ga inda su ka afka.

Idan kunne ya ji..........

Lambun Ma'aurata Team

Comments

Popular posts from this blog

HUTSUN MIJI DA MACE MAI TSIWA

GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA

MATSALAR SHAYE-SHAYE