Posts

ƳAM BIYU NA GAISHE KU

Image
ƳAN BIYU NA GAISHE KU Akwai hanyoyi da dama waɗanda mai gida zai iya taimakawa matarsa wajen rainon yara: Za ka iya ɗaukar ma ta yaran yayinda ita kuma ta ke gudanar da sauran ayyukan gida. Wasu kan yi ƙorafin cewa yaran su na yi musu ƙiwa. To dalilin kuwa shi ne tun farko mijin ya riga ya sakarwa matar don haka shi kuwa yaro ya ke ganin tsohon nasa ma a matsayin wani baƙo da zai iya cutar da shi don haka su ke tsala ihu da sun ji su a hannun da bai saba riƙe su ba. Za kuma ka iya lura da sauran aikace-aikacen gida yayinda ita kuma uwar yaran ta ke kula da su. Shin Ko ku san cewa idan aka bari yara su ka saba da cewa kuka ne kaɗai hanyar da su ke isar da saƙo ga iyayen su idan wani abu na damun su, ku ne a ƙarshe za ku sha fama da rigimar su? Hatta goya yara miji zai iya koya ya dinga jijjagasu har a samu su yi barci. Akwai namijin da.kukan yara ya ke  duguzuma shi. To irin waɗannan mazajen ya zame musu ma dole ne su fara koyon yanda ake raino idan ba haka ba kuwa duk sanda aka ce ...

GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA

GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA Shin ku na cikin magidanta da su ke cacar baki a gaban yaran su? Idan ku na cikin masu yin hakan to akwai gagurmar matsala da saƙon da ku ke isarwa zuwa gare su. Yawanci dai bincike ya nuna cewa duk ma'auratan da su ke irin wannan halayyar to su ma Idan aka tsawaita bincike tasowa su ka yi su ka ga na su iyayen su na aikata irin wannan mummunan halin. Kun ga kenan hanya ɗaya da za'a iya takawa wannan abu burki shi ne ta dakatar da abin daga kan ku kafi ku cigaba da shuka shi ya na ƙara tofon girma da yaɗo a zukatan ƴaƴan ku inda su ma za su aikata hakan ga ƴaƴan wasu a nan gaba. Babu wata matsalar da tattaunawa ba za ta iya magance ta ba.

FARIN CIKIN IYALI

Image
Farin cikin iyali shi ne ya ke samar da farin cikin a al'umma baki daya. Wannan ya na faruwa ne saboda kowace al'umma ta na farawa ne daga daidaikun iyalai wadanda idan an hada su waje guda su ke samar da al'umma. Ma'aurata a cigaba da kasancewa cikin farin ciki da fahimtar juna banda daga murya a gaban yara ko cin zarafin juna. Shi yaro fa kamar biri ne, duk abinda ya gani to daga gare ku to shi koya ya ke kuma ana nan wata rana sai ya kwaikwaita domin ya na daukar iyayensa ne a matsayin wani madubin dubawa. Ku kasance cikin farin ciki da samun nutsuwa da juna!

NUNA KULAWA DA ƘAUNA GA ƘANANAN YARA

Nunawa ƙananan yara kauna da matukar kulawa a lokacin da su ke tasowa ya na da muhimmaci da tasiri a yanda za su dinga mu'amalantar al'umma su ma yayinda su ka girma su ka shiga cikin sauran jama'a. Idan yaro ya taso cikin hantara, kyara, gwalewa da fushi da jin fusatattun kalamai, to haka nan shi ma zai zama a cikin al'umma. Idan kuma a daya bangaren kauna da tausayawa juna ya taso ya na gani tun daga gida, to shi ma abinda zai fi baiwa mahimmanci kenan duk lokacin da ya isa shiga cikin jama'arsa.

GIDAN AURE MAI CIKE DA HAYANIYA

GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA Shin ku na cikin magidanta da su ke cacar baki a gaban yaran su? Idan ku na cikin masu yin hakan to akwai gagurmar matsala da saƙon da ku ke isarwa zuwa gare su. Yawanci dai bincike ya nuna cewa duk ma'auratan da su ke irin wannan halayyar to su ma Idan aka tsawaita bincike tasowa su ka yi su ka ga na su iyayen su na aikata irin wannan mummunan halin. Kun ga kenan hanya ɗaya da za'a iya takawa wannan abu burki shi ne ta dakatar da abin daga kan ku kafi ku cigaba da shuka shi ya na ƙara tofon girma da yaɗo a zukatan ƴaƴan ku inda su ma za su aikata hakan ga ƴaƴan wasu a nan gaba. Babu wata matsalar da tattaunawa ba za ta iya magance ta ba.

MATSALAR TATTALIN ARZIƘI

MATSALOLIN DA SU KA ADDABI RAYUWAR AURE (cont.) 8) MATSALAR TATTALIN ARZIKI Allah shi ne cikakken Mawadaci kuma Abin Godewa. Duk sauran mutane kuwa masu buƙatuwa ne zuwa gare Shi. Wasu lokutan aure kan zo da camfi ko afkuwar matsalar ƙuncin rayuwa sanadiyyar nauyaye-nauyayen da su kan hau kan magidanta da kuma rashin samun ƙarin wasu hanyoyin damun kuɗaɗen shiga sannan da rashin tsarin kasafin kasashe kuɗaɗe da mu ke yi a yawancin lokuta. Wa su su fara canfa amarya da cewa mai farar ƙafa ce da makamantan waɗannan zantukn. Wannan na zama babbar barazana idan aka sami rashin fahimtar yanayin rayuwar musamman da ga ɓangaren mata. Sau da yawa matsalar matsin tattalin arziƙi da ƙuncin rayuwa ta janyo macewar aure bida adadin. Wani magidancin ma idan garin ya yi masa zafi arcewa ya ke ya bar iyayen yarinya da ɗaukar nauyinta, idan abin ya tsananta kuma alƙali ya bata gaiba a kashe auren ɗungurungun. Shwara ga matan...

MATSALAR SHAYE-SHAYE

MATSALOLIN DA SU KA ADDABI RAYUWAR AURE (cont.) 7) MATSALAR SHAƳE-SHAYE A sannu a hankali dai shan miyagun ƙwayoyi da zuƙe-zuƙen hayaƙi kala-kala na neman zama ruwan dare tsakanim matasan wannan yanki. Wannan ya sanya matsalar ta afka har gidajen aure sakamakon daman ma'aurata na shaye-shayen su tun kafin auren ya riga zame mu su jiki inda ba za su iya rabuwa da shi cikin sauƙi ba. Babban abin takaicin ma shi ne yanda shaye-shayen miyagun ƙwayoyin kusan ya ke neman komawa ga mata. Yayinda su ka karɓe shi ka'in da na'in. Wasu ana yaudarar ne da cewa ya na kwantar da hankali da kuma ƙara kyau. Wasu kuma su na sha ne da niyyar yaye damuwa ko ƙara sha'awa a ƙarshe su ɓuge ta zama ƴan maye cikakku. Shari'ar Islama ta zo ne dan kare wasu mihimman abubuwa guda biyar na rayuwar ɗan adam cikin su harda hankalinsa saboda matuƙar himmancin sa. Idan mutum ya zama ba shi da hankali, to wata dabbar ma ta fi shi domin su da...