MATSALAR TATTALIN ARZIƘI

MATSALOLIN DA SU KA ADDABI RAYUWAR AURE (cont.)

8) MATSALAR TATTALIN ARZIKI
Allah shi ne cikakken Mawadaci kuma Abin Godewa. Duk sauran mutane kuwa masu buƙatuwa ne zuwa gare Shi. Wasu lokutan aure kan zo da camfi ko afkuwar matsalar ƙuncin rayuwa sanadiyyar nauyaye-nauyayen da su kan hau kan magidanta da kuma rashin samun ƙarin wasu hanyoyin damun kuɗaɗen shiga sannan da rashin tsarin kasafin kasashe kuɗaɗe da mu ke yi a yawancin lokuta. Wa su su fara canfa amarya da cewa mai farar ƙafa ce da makamantan waɗannan zantukn. Wannan na zama babbar barazana idan aka sami rashin fahimtar yanayin rayuwar musamman da ga ɓangaren mata.

Sau da yawa matsalar matsin tattalin arziƙi da ƙuncin rayuwa ta janyo macewar aure bida adadin. Wani magidancin ma idan garin ya yi masa zafi arcewa ya ke ya bar iyayen yarinya da ɗaukar nauyinta, idan abin ya tsananta kuma alƙali ya bata gaiba a kashe auren ɗungurungun.

Shwara ga matan da mazajen su su ka shiga wani hali na rayuwa ita ce su daure kada su dinga matsawa kan duk wasu abubuwan da ba dole ba ne a rayuwa. Su dinga nunawa mazajen su tausayin su da jinƙan su a fili, tareda taimaka mu su da duk abinda za su iya iya bakin ƙarfin su.
Duk macen da ta tausayawa mijinta a halin ƙunci zata sha mamaki idan daga baya Allah ya ƙara wadata su domin ɗan halak ba ya manta halacci. Wannan ya sa ake ganin wasu manyan attajirai kamar su na fifita matarsu ta lalle akan kowace mace saboda shi kaɗai ya san irin halaccin da ta yi masa lokacin da ake cikin halin fatara. Idan kuwa aka gamu da mai auri saki ma za'a ko da yaushe a cikin sauran ukun ake tarawa da ɗebewa amma ita ta ƙunshi ta na nan mutu ka raba takalmin kaza.

Kada ki dinga nuna ido ƴar uwa, ace komai ana jira sai miji ya nemo ya kawo koda kuwa yana cikin mahuyacin hali amma ke kuma kina da wadatar da za ki iya maganta wannan matsalar.
Koda yaushe mu dinga tuna cewa Allah ya kawo aure ne domin mazaje su dinga samun natsuwa da ga mata sannan kuma ya sanya ƙauna da jinkai tsakanin ma'auratan.

Allah don girma da sirrin da ke cikin  sunayenka Arrazzaqul-Fattahu Al-wasi'ul-Hakeemu ka yayewa duk ma'auratan da su ke cikin ƙuncin rayuwa saboda karayar arziƙi da kuma halin tsadar kayan masarufi da ake ciki a halin yanzu.
Mun gode sai kunji mu a wallafa ta gaba da ikon Allah.

@Lambun Ma'aurata

Comments

Popular posts from this blog

SOYAYYA BATA RIƘE AURE

HUTSUN MIJI DA MACE MAI TSIWA

GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA