NUNA KULAWA DA ƘAUNA GA ƘANANAN YARA

Nunawa ƙananan yara kauna da matukar kulawa a lokacin da su ke tasowa ya na da muhimmaci da tasiri a yanda za su dinga mu'amalantar al'umma su ma yayinda su ka girma su ka shiga cikin sauran jama'a.

Idan yaro ya taso cikin hantara, kyara, gwalewa da fushi da jin fusatattun kalamai, to haka nan shi ma zai zama a cikin al'umma. Idan kuma a daya bangaren kauna da tausayawa juna ya taso ya na gani tun daga gida, to shi ma abinda zai fi baiwa mahimmanci kenan duk lokacin da ya isa shiga cikin jama'arsa.

Comments

Popular posts from this blog

HUTSUN MIJI DA MACE MAI TSIWA

GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA

MATSALAR SHAYE-SHAYE