ƳAM BIYU NA GAISHE KU
ƳAN BIYU NA GAISHE KU
Akwai hanyoyi da dama waɗanda mai gida zai iya taimakawa matarsa wajen rainon yara:
Za ka iya ɗaukar ma ta yaran yayinda ita kuma ta ke gudanar da sauran ayyukan gida. Wasu kan yi ƙorafin cewa yaran su na yi musu ƙiwa. To dalilin kuwa shi ne tun farko mijin ya riga ya sakarwa matar don haka shi kuwa yaro ya ke ganin tsohon nasa ma a matsayin wani baƙo da zai iya cutar da shi don haka su ke tsala ihu da sun ji su a hannun da bai saba riƙe su ba.
Za kuma ka iya lura da sauran aikace-aikacen gida yayinda ita kuma uwar yaran ta ke kula da su.
Shin Ko ku san cewa idan aka bari yara su ka saba da cewa kuka ne kaɗai hanyar da su ke isar da saƙo ga iyayen su idan wani abu na damun su, ku ne a ƙarshe za ku sha fama da rigimar su?
Hatta goya yara miji zai iya koya ya dinga jijjagasu har a samu su yi barci.
Akwai namijin da.kukan yara ya ke duguzuma shi. To irin waɗannan mazajen ya zame musu ma dole ne su fara koyon yanda ake raino idan ba haka ba kuwa duk sanda aka ce matarsu ta suntulo ƴan biyu ina tabbatar mu ku da cewa ƙarshen fa ba zai yi musu kyau ba, domin kuwa su ƴan biyu komai na su lokacin guda su ke haɗa kai su yi ta yi hatta kukan ma.
Allah ya sa a faɗaka.
Comments
Post a Comment