MATSALAR SHAYE-SHAYE

MATSALOLIN DA SU KA ADDABI RAYUWAR AURE (cont.)

7) MATSALAR SHAƳE-SHAYE

A sannu a hankali dai shan miyagun ƙwayoyi da zuƙe-zuƙen hayaƙi kala-kala na neman zama ruwan dare tsakanim matasan wannan yanki. Wannan ya sanya matsalar ta afka har gidajen aure sakamakon daman ma'aurata na shaye-shayen su tun kafin auren ya riga zame mu su jiki inda ba za su iya rabuwa da shi cikin sauƙi ba.

Babban abin takaicin ma shi ne yanda shaye-shayen miyagun ƙwayoyin kusan ya ke neman komawa ga mata. Yayinda su ka karɓe shi ka'in da na'in. Wasu ana yaudarar ne da cewa ya na kwantar da hankali da kuma ƙara kyau. Wasu kuma su na sha ne da niyyar yaye damuwa ko ƙara sha'awa a ƙarshe su ɓuge ta zama ƴan maye cikakku.

Shari'ar Islama ta zo ne dan kare wasu mihimman abubuwa guda biyar na rayuwar ɗan adam cikin su harda hankalinsa saboda matuƙar himmancin sa. Idan mutum ya zama ba shi da hankali, to wata dabbar ma ta fi shi domin su dai dabbobi haka nan Allah ya halicce su da daidai hankalin da za su iya tafi da rayuwar su ta yau da kullum kai kuwa ɗan Adam idan ka rasa hankali musamman sakamakon shaye-shayen da ka jefa kanka, to tabbas za ka zama kafi dabba lalacewa.

Yanda shaye-shaye ke shafar zamantakewar aure kuwa shi ne ta hanyar damalmala yanayin zaman da tashe-tashe hankulan da ba sa ci ballantana su cinye. Shaye-shaye ya kan sa mutum ya zama mai zargi da saurin fusata. Waɗannan matsaloli kuwa na haifar da tarzoma a gidajen aure.
Idan magidanta su na shaye-shaye zai janyo ɗaukewar sha'awa ga mata sannan kuma ya kawo saurin inzali ga maza. Sannu a hankali sai ka ji rigima ta ɓarke nan da can.

Hakazaliƙa shaye-shaye ya na haifar da matsalar dukan da faɗan dambe a gidajen aure. Za ka ga ma'aurata su na son juna  amma ƙwaya ta sanya za su iya fita da ga hayyacinsu har su iya ma jibgar madoyan du cikin halin buguwa.
Wasu a irin wannan halin har su na kaiwa da ɗaukar makami su hallaka abin ƙaunar su da hannun da su ke tarairayar su a baya.

Idan ana son shawo kan wannam matsala, to dole ne iyaye su zama masu sanya ido da lura da duk wasu sauye-sauyen da su ka gani a wajen yaran su matasa tun kafin suyi nisa. Wa su da ga cikin alamun da iyaye ya kamata su ankara da su sun haɗa da: yawan barci, zama wajen ɗaya ayi shiru bayan matashi bai saba hakan ba, yawan saurin fushi, ƙazanta, sauya sabbin abokai marasa tarbiyya, ɗauke-ɗauke, dss.
Da zarar Allah ya sa an lura da wuri to in Allah ya yarda shawo kan matsalar zai zo da sauƙi, amma idan shaye-shaye ya bi jinin matasa to fa sai dai Allah ne kawai magani.

Duk matashin da ya ke son daina shaye-shaye kuwa zai iya ta hanyar rabuwa da miyagun abokan da su ke wannan harkar tare, da kuma tsarin samun wani abin yi wanda zai dinga ɗauke musu kewa, da kuma yawan anbaton Allah da tsaida sallah ba wasa da barin wasu ayi wasu a hankali ita sallar zata hana shi aikata duk wata alfasha da aikin munkari kamarbyanda Allah ya bada tabbaci a littafin Sa mai Girma.

Wani malami kuma ya bayyana wata aya a Suratul-Ma'ida wadda ake rubutawa ko a tofa a ruwan zam-zam a baiwa duk masu shaye-shaye su sha da kyakkyawar niyya idan Allah ya so ya yarda za'a dace:
"INNAMAL KHAUMARU WAL MAISIRU WAL ANSABU WAL AZLAMU RIJSUN MIN AMALISSHAIƊAINI FAJTANIBOOH"
To iya waqafin nan za'a tsaya sai a sake karantawa ko rubutawa har ƙafa bakwai 7.
Wanda duk baya shan muyagun ƙwayoyi ya kiyayi duk wata yaudarar abokai, ƙawaye ko samarin da su ka halaka kuma su ke ƙoƙarin hallaka wasu ta hanyar yaudarar su da ƙarerayen banza kan miyagun ƙwayoyi. Waɗanda kuma aka jarrabe su da afkawa wannan matsalar masu auren da matasan samari da ƴan matan kuma duk Allah ya dawo mana da su kan hanya madaidaiciya.

Sai kun ji mu a matsala ta gaba wato ta takwas (8).
Mun gode.
@lambunmaaurata

Comments

Popular posts from this blog

HUTSUN MIJI DA MACE MAI TSIWA

GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA