MATSALAR RASHIN IYA GIRKI

MATSALOLIN DA SU KA ADDABI RAYUWAR AURE (Cont.)

6) MATSALAR RASHIN IYA GIRKI

Idan kuna biye da mu wannan gagarumar matsalar ita ce ta shida a jerin da muka dauko na tattauna matsalolin da du ke addabar zamantakewar aure yanzu a kasar Hausa.

Ga duk wadanda su ke zaune a birane za su iya lura da wani abin mamaki, idan su ka fita unguwa su ka gifta ta gidajen sayarda abinci. Abu na farko da za ku iya lura da shi shi ne manya manyan motocin alhazawa sun zo cin abinci. Ko kun taɓa tsayawa kunyi tunanin cewa meye ya ke kawo babban mutum da wadatar sa da komai siyan abinci a gidan cin abinci? Amsa anan ita ce: Abincin gidan ne baya ciyuwa sai dai ayi kara a dan ci kadan ace wai an koshi. Kunga kuwa dole idan an fito waje a nemi wajen da za'a dan sami ƙwalam da  maƙulashe mai daɗi.

Wannan matsala dai kullum sai ƙaruwa ta ke. Waɗancan alhazan da ke zuwa godajen cin abinci bayan sunfi ƙarfin komai fa su na yakana ne kawai. A wasu gidan kullum cikin riƙici ake kan cewa mai gida ya bada isasshen kuɗin cefane amma girki da ga loma ɗaya sai aji ya na neman dawowa saboda tsabar ƙwamacalar matan ƙarshen zamani ta rashin ilimin sarrafa abinci ya bada ma'ana.

Babban dalilim da ya ke jawo ƙaruwar wannan matsala kuwa shi ne: shagwaɓa da sunan gata da iyaye mata su ke nunawa ƴaƴansu mata a wannan lokacin.  A zamanin da can a ƙasar Hausa yarinya tun tana ƴar ƙarama ake fara nuna mata hanyar madafi da kuma dabarun gyaran kayan abinci da hana su lalacewa. Wa su lokutana  ma a ɗan ɗebi kayan abinci a bata ta fara jagwalgwalawa da kanta ana ɗan yi mata gyare-gyare.

Wa su ƴan matan ma tun su na yin tuwon ƙasa a tukunyar ƙasa ta wasa har su fara gwada irin su wainar fulawa da sauran su da wasa da wasa kafin ayi aune sai a ga sun ƙware.
Duk wanda ya ɗan gota shekara ashirin ko sama ya san wannan al'adar. Sai ga shi kuma Allah ya kawo mu zamanin 'son' ƴaƴa na banza da sangarta su saboda boko da shigowar baƙin al'adu da kuma dogon burin cewa ma ai gidan hutu za ta je ba lallai ne ma ita za ta dinga yin girkin ba ma aka daina nusar da ƴan mata dabarun sarrafa kayan cefane su zama lafiyayyen girki.
Wata yarinyar taliyar ƴan yaye ma sai ta bugo waya wai a koya mata:  "Bayan an dafa ruwa zafin sai me kuma momcy?" Wannan ce daya daga cikin tambayoƴin da wata amarya ƴar gidan ƴan gayu ta yi wa gyatumar ta wadda ta sangarta ta bata iya komai ba a kitchen har a ka kai ta ɗaƙin aure. An wayi gari za'a karya kumallo amma ga shi bata iya komai ba sam sam.
To a irin haka ne fa da an sami hutsun miji sai aji fitina ta fara kunnowa tun kafin a gama cin Talata da Larabar.

Sakacin iyaye ne musamman mata na cewa ba za'a nunawa yara yanda ake girki ba saboda kawai su na karatun boko wannan babbar illa ce. Ace wai yarinya tun tana shekara uku an kwasa an kaita raino wajen arna da sunan karatu ba za ta dawo gida ba sai wajen karfe uku na yamma kuma tun bakwai ta fita da ga gida tsawon kawanakin shekara 365 kwata-kwata ba kwa shafe cikakkun wata uku tare da ga safe har dare to ta yaya za'a taɓuƙa abin arziki kuwa? Dole ne iyaye su ware lokutan koyawa ƴayan su mata, kai har mazan ma girke-gitke. Domin idan namiji ya iya girki ba ƙaramin anfani wannan zai masa ba idan yayi aure ta hanyar taimakawa iyalinsa da kuma yanda hakan ya ke zama wani garwashin da ya ke ƙata rura wutar romansiyya tsakanin ma'aurata.
Gyara kayanka dai Hausaa na cewa baya taɓa zama sauke mu raba. Idan ki ka ɓata ɗan ƙaramin lokacin ki wajen horar da ƴaƴanki dabarun girke-gitke to kin magance musu matsalar aure kashi 30-50 bisa ɗari a ire-iren matsalolin da ake samu a zaman aure.

Abinda ya sa ake auro muku wasu ƙabilun maƙota da aka san sun ƙware a iya girki kenan sannan ku zo kuna ƙorafin wai cewa su na korar kishiya da asiri da makirci. Ƙe ma idan kin kula da tallen miyar ki yanda ya kamata sai dai kuyi gogayya ko da kuwa da ga birnin Santanbul aka auro ta.

Allah ya sa mu gane. Sai mun haɗu a matsala ta 7 da ikon Allah Mai Duka. Mun gode.

@Lambun Ma'aurata

Comments

Popular posts from this blog

HUTSUN MIJI DA MACE MAI TSIWA

GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA

MATSALAR SHAYE-SHAYE