Shin mace za ta iya bayyana soyayyar ta ga namiji?

SHIN MACE ZA TA IYA FURTA KALMAR SO GA NAMIJI? Wannan tambaya ce mai matukar wahalar amsawa ga mata. Iska dai ta dade ta na wahalar da mai kayan kara tsawon zamunana. A zamanin da can idan budurwa ta na son suarayi ta na yi masa nuni ne cikin nishadi a dandali yayinda ta fito farfajiyar gada za ta bada waka. Akan ji yarinya ta na koda nau'in sanai'ar gidan su mijin ta da fidda a matsayin na karfen nata. Da ga nan kuma sai magabata su Ankara su shigo maganar. Akwai misalan irin wannan na da dama a cikin wasu wakokin dandali da adabin baka ya adana ma na su har mu ka san su a yau. Amma da zamani ya nisa kuma bakin al'adu da ilimin yamma ya shigo ma na sai abubuwan su ka sauya. Gadar ma yanzu wata ba ta san yadda ake yi ba. A halin yanzu dai yan mata na ganin cewa wata mummunar faduwa ce ko zubar sa aji ace wai mace ta nemi soyayyar saurayi. Wannan girman kan da zurfin cikin ko Kuma na ce nauyin bakin ya dade ya na sanya yan mata su na bugewa da auren mijin da ba sa kauna kwata-kwata saidai kawai a zauna a hayayyafa har a tsufa ayi masa takaba, amma fa babu ko digon kauna digo daya a zuciyar su. A rashin tayi dai Hausawa su ka ce akan bar arha. Kuma a rashin Kira Karen bebe ya bata. Wannan a bangaren tsohuwarsa al'ada Malam Bahaushe fa kenan. Idan Kuma mu ka kalli bangaren abubuwan da su ka zo a addini, babu inda wani hani ya zo kan idan mace ta ga wanda kyawawan dabi'un sa su ka kayatar da ita da ta aika masa ko kumu ta tunkare shi da batun soyayyar da za ta kai su har zuwa ga aure. Za mu iya tuna kissar Annabi Musa lokacin da ya bar Misra ya shiga Madyana a inda ya tarar da wasu yan mata yayan wani dattijo har ma dai ya taimakawa mu su su ka shayar da dabbobin mahaifin su. To ai yayinda aka tura daya daga cikin su ta kiranI shi domin ya gama da shi, ta Lura da amana da kuma kunya sa har ma ta nunawa mahaifinta cewa ayi duk kokarin da za'a yi ayi masa sakayya irin wadda ta kama ta ayiwa mutum mai Karfi Kuma amintacce. Nan da nan dattijo nan ya lura da abinda yar sa ta ke nufi inda ya nemi ya bashi auren ta bisa sadaukin zai masa kiwon dabbobin na tsawon shekaru takwas idan kuma ya cika goma to ya kyautata. A karshe a kyawun hali na Annabawa ya cika masa goman. Ga Kuma babban misalin yanda Nana Khadijatul-Kubra ta ji gaskiya, amana, kyawawan dabi'u da Kuma abubuwa da Bawan ta Maisara ya ji Kuma ya gani a yayinda tafiya da dawowar su da ga Sham. Da kuma abinda Nastura malamin nan na Sham ya tabbatar masa na Annabtarsa. Sai Nana Khadija ta je wajen Dan uwanta wanda su ke yan maza zar wato Waraqa Dan Naufal wanda shi zaman masanin Attaura ne inda ya kara tattabatar da cewa duk abubuwan da Maisara ya bata labari ba sa faruwa sai ga Annabi saboda haka ya kwadai ma ta cewa ta nemi ya aurenta sabaoda kada wannan babban alheri ya kubucewa Gidan su. Nana Khadija ta kasance ta na aikatawa wata kawarta ga Annabi ASW har dai zuwa lokacin da ya amince da taimakon Baffansa Abu Talib aka nema masa auren Nana Khadija a hannun Baffansa Umar Dan Asad. Idan Kuma ke kinfi ganin yan kungiyoyin 'what man can do...' da mahimmaci, to ki kalli hirar da aka yi da A'isha Yesufu salamburutin EndSARS (wato mai Hijabi) . A wata hira da aka yi da ita ta bada cikakken labarin yadda ta lallaba tayi wuf da mai gidan ta inda ta bada labarin cewa har ma daukar sa ta ke aje shan icecream. Saboda haka babu wani laifi idan budurwa ta ga wanda ya kwanta mata a zuciyar ta son ta bayyana masa soyayyar ta baro-baro, ko ta ishara ko kuma ta aikawa da yan sako. Abinda ya sa nayi wannan rubutu kuwa shi ne maganar wani faifan bidiyon da wata yar uwa ustaziya ta ke yiwa yan mata nasiha cikin jan hankali kan su tsaya su lura da dabi'un duk suarayin da yayi musu su aikawa masa da sakon su na kauna ba tareda da jin wani tsoro ba. Bayan sakar wancan faifan bidiyon ne sai wasu yan mata su ka dinga izgili da fada mata bakaken maganganun da sam ba su dace ba kawai don tayi musu nasihar gyaran kayan ka. To ke ma mai karanta wannan rubutu da ke na ke: idan dai ba matsoraciya ba ce ke, mai cike da girman kai, kuma mai kayan karan da iska ke ta wahalarwa, to dai na san akwai wani dan suarayin da kI ka zaba amma wai kina jiran wai sai ya bayyana miki, to wallahi ki daure ki lallaba ta duk dabarun ki na mata ki tabbatar a karshe dai kinyi WUF da shi zuwan dakin ki na aure. Allah ya sa mu gane. Lambun Ma'aurata

Comments

Popular posts from this blog

HUTSUN MIJI DA MACE MAI TSIWA

GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA

MATSALAR SHAYE-SHAYE