MATSALOLIM DA KE ADDABAR GIDAJEN AURE

4) Jahiltar Auren Kansa
Yawancin matasa masu shirin yin aure fa ba su san komai ba game da aure. Ana maganar aure abinda ke fara faɗowa ransu shi ne alaƙar da ake yi a wancan ɗakin na karshen guda ko kuma turaka.
Babu wanda zai zaunar da su ya faɗa musu nauyaye-nauyaye da ke cikin auren har a zo a shigo da ka sai kuma a fara jin ƙorafe-ƙorafe nan da can tun kafin a gama cin Talata da Laraba.
Abu mafi ban mamaki ma shi ne hatta ana daf da shigar da ango da amarya ɗakin aure ba abinda iyaye ke mayar da hankali sai 'gyaran jiki' .Shi kuwa a ɓangaren ango ba wanda ma ya damu da na sa matsalolin sai abokai ne kawai za su yi ta bashi shawarwari na banza da shan ƙwayoyin ƙarin ƙarfi aƙarshe azo ayi haihuwar guzuma a daren farkon da marubuta littafan Hausa su ka gama kwarzanta shi da labarun ƙanzon kurege.

Haƙiƙanin aure ba fa iya alalar da ke tsakanin maji da mata ba ne kawai. Akwai sauran abubuwa da dama kamar nuna kulawa ga juna, tausayin juna da jinƙan juna da kuma taimakekeniya a tsakanin juna.
Saboda yawaitar ire-iren waɗannan matsaloli ne fa yanzu a wasu garuruwan aka fara bubbuɗe makarantun koya zaman aure da dabarun sana'o'i. Ire-iren waɗannan makarantu za su taimaka matuƙa gaya wajen rage ko kawo ƙarshen wancan jahilci da mu ke da shi akan ainihin menene ma auren kansa.

Akwai amaryar da taliyar ƴan yaye kawai ta iya dafawa amma an kaita gidan mai gyaran jiki tayi kwanaki ana banka mata wasu abubuwan da wasu ma kan iya illatata kafin akai ga yin auren. Sabida idan mace ta banki 'kayan gyara' kamar yanda su ke kuran su wata jini ne ya ke ɓalle mata wanda kuma ba lokacin sa ne yayi ba. Ga ango shi kuma ya biyewa shawara wawayen abokai shima ya je ya banko na sa ƙwayoyin da jiƙe-jiƙen kwai sai dai ku ji rikici ya ɓarke tun a daren farkon da aka ciwa dogon buri.

Ko rabin rabin makudan kuɗin da ake kashewa wajen shafe-shafen gyatuma raɗau da ake yiwa amarya, wanda kuma za'a zo a wanke shi a banza da wofi ya isa a kai ta tayi makarantar koyan dabarun zaman aure da sana'oi amma ina......?

Hausawa na cewa da ga na gaba ake gane zurfin ruwa. Kamata yayi iyaye da sauran magabatan ma'aurata su jajurce wajen nusar da makusantan su yanda aure yake. Ba wai kawai sai ranar biuɗar kai a dinga nanata mui kalam ɗaya har sai ta baiwa ango da amaryar haushi ba 'ayi haƙuri, sai fa anyi haƙuri.......! Mutuwa akai da za'a dinga wani zancen ayi haƙuri?

Su fa angwayen abinda ma ya fI ba su haushi da  mamaki shi ne wane irin haƙurin kuma  ake ba su bayan su da su ke ganin auren soyayya ne su ka yi?
Babbar matsalar da iyaye ba sa ganewa ita ce ba kalmar haƙuri ma ya kamata ayi anfani da ita a can tunda farkon. Idan abu ba zai faɗu a kalma guda ɗaya ba ba sai ayi jumla ko jumloli ba domin bayyana shi?  Duƙ abonda zai iya kawo matsala ko tarnaƙi ga aure to kamata yayi ayiwa tufkar hanci tun wuri ba wai sai abu ya ta'azzara ba azo ana zance da karkata kai.

Aure sai mai juriya jajurtacce, wanda su ka yarda cewa ita soyayya sadaukarwa ce. Domin kuwa a soyayya  ba komai za ka iya hasashen sa kuma ya zama ƙa samu ɗari bisa ɗari ba ragowa sai a cike shi da wannan sadaukarwar ta masoyan asali.
A biyo mu a rubutu na gaba domin jin matsala ta 5 wadda kullum ta ke yi wa aure kisan mummuƙe ba tare da an tsaya an tunkare ta da nufin maganta ta ba wato: matsalar Rashin Gyaran Turaka.
Sai kun ji mu mun gode.
@lambunmaaurata

Comments

Popular posts from this blog

HUTSUN MIJI DA MACE MAI TSIWA

GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA

MATSALAR SHAYE-SHAYE