MATSALAR RASHIN GYARAN TURAKA

MATSALOLIN DA KE ADDABAR AURE (Cont.)

5) MATSALAR RASHIN GYARAN TURAKA

Wannan matsala ce da ke da wahalar sha'ani wadda ita ma ta dade tana yiwa aure kamshin mutuwa ko ma hallaka shi gaba daya. Ma'aurata ko da a junan su na kunyar tattauna wannan batu ballanta idan abin ya ci tura a sako magabata, yayinda a karshe dai ta ke zamewa sawarwarin macewar aure.

Ba za ku san da matsalar rashin samun gamsuwa tsakanin ma'aurata ba musamman mata sai ana gabatar da wani shiri a radiyo inda da zarar an bada damar aiko da sakonni za ku sha mamakin irin batutuwan da ke cike da turnikin gajimaren bakin ciki da ma'aurata ke kunsa kan wannan batu ya na ta fitowarsu dalla-dalla.

Ba bu abinda mace ta tsana irin mijinta ya bar ta a kan hanya bayan an tsokanota. Wannan yana zame  musu dandani haukaci ko kuma nace  cankackaare inda ya ke sanya musu fushi da ma tsanar mu'amalar auren ma baki daya.

Shi kuma mijin a nasa bangaren  yawanci ma shi bai san ta shiga wani hali ba saboda gaskiyar magana mata suna yin kwauron baki  wannan harkar. Wannan kuma kan faru ne saboda wasu mazan su kan fusata idan iyali su su ka ce mu su ba su koshi ba. Saboda nimiji yana da jin Kansa cewa ya isa ba kuma ya son gazawa ko kadan.

Idan mata su ka hadu a gidan biki ko suna,  ba abu mafi mahimmanci da su ka fi tattaunawa sama da wannan. Wata ta shiga karya idan ta ji yan uwa ta na nuna cewa wai su mowoyin mata saboda yadda  ake ba su kulawa da tarairaya, yayinda wata kuma za ta ja gefe ta na tuna tata turakar mijin da irin bakin cikin da take kunsa a duk sanda aka gamu.

Haka nan kuma su ma mazan ba kowanne nimiji ne zai iya bude baki ya fadawa iyalinsa cewa: shi fa ba inda ya je bayan ya kasance ta ba. Wannan a karshe ya kan jnayo sanewa da kuma gundurar juna ba tareda  ma'auratan kan su sunyi aune ba.

Wasu da ga cikin abubuwan da ke janyo rashin samun gamsuwa a turakar sun hada:
Wasu cutuka kamar sanyi ko cutar sukari.
Cutar Damuwa
Shan miyagun kwayoyi
Rashin barci
Matsalolin kwakwalwa
Saurin inzali
Tsufa
Wadannan kadan ke nan da ga abubuwan da ke janyo rashin samun abinda ake muradi  a turaka ko ga mijin ko kuma ga matar.
Maraba sun ce ana bukatar akalla minti biyar zuwa goma ana tabukawa kafin ace kowanne bangare ya kai mako shi.

Za'a iya cimma wannan ko sama da hakan ta hanyoyi kamar haka: wasannin somin tabi, motsa jiki musamman ma atisayen Kejal ga maza da mata, zaman harden yoga, cin abinci mai kumbura sha'awa kamar kayan marmari, dabino, zuma, madara, kwai, kankana, aya, ridi, kwakwa da madara, muruci, mangwaro DSS, yawan shan ishasshen ruwa da kuma anfani da salon kwanciya daban-daban a dare daya a turaka.

Hakazalika, idan ba'a kai ga debo ruwan a rijiya ba sai a bari idan aka huta bayan anyi wanka da asuba kuma sai a sake bawa juma kulawar da ta dace.
Yawan kusantar juma akai-akai musamman ma idan akwai wannan matsalar ya kan daidaita al'amuran cikin sauki.

Wannan dai matsalar ce mai wuyar sha'ani da ba Kasafai kuma ake zama ayi batu akanta ba a wannan yanki namu saboda tsarin addini da kyawawan dabi'un mu, amma fa abin ya fara yawa duk da cewa ba magidnatan da za su sako magabata kan wannan batu saboda tsoro da kuma kunya.

A irin wannan hali ne kuma wasu mazan ke karo aure bayan sun san matsayin sha'awar su koda ta gidan dai  hankuri ta ke wai kuma su ma auri yan matan internet generation wadanda idanun su su ka bude tarwai sai Kama a fara labarin dalla-dalla  tsakanin kawaye ai ba cikakken namiji ba ne. Allah gafarta malam kada ka ce wai dole sai kaima ka kara aure saboda kawai wadanda ku kayi aure lokaci guda, ko abokan kuruciya ko na kasuwa sun kakkara. Maidai daki shi yasan inda ya ke yi masa zuba ko son gudun jin kunyar amaren yanar gizo-gizo.

Ga mata kuma ga labarin wata tsohuwa da jikarta nan ya ishe ku ishara:
Wata amarya nada  kaka da take yawan nanata mata cewa: idan kika iya gyaran gado to babu abinda mai gidanki ba zai miki ba".  Ita wannan amarya saboda kuruciya wai ta dauka gyaran shinfidar gado ake nufin, saboda haka kullum sai ta gyaran shinfidar fesfes ta yi tsantsan ba inda ya zame. A karshe dai wannan har tsohuwa ta gane jikarta nan tata fa bata gane me ake nufin da gyaran gadon nan ba sai da wannan tsohuwarsa ta cire alkunya ta fada mata baro-baro.
Allah ya warwarewa dum masu wata matsalar a gidajen su na aure ya sa kuma gidan auren ya zame musu tafarkin samun aljanna madaukakiya.

@lambunmaaurata

Comments

Popular posts from this blog

HUTSUN MIJI DA MACE MAI TSIWA

GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA

MATSALAR SHAYE-SHAYE