Shin mace za ta iya bayyana soyayyar ta ga namiji?
SHIN MACE ZA TA IYA FURTA KALMAR SO GA NAMIJI? Wannan tambaya ce mai matukar wahalar amsawa ga mata. Iska dai ta dade ta na wahalar da mai kayan kara tsawon zamunana. A zamanin da can idan budurwa ta na son suarayi ta na yi masa nuni ne cikin nishadi a dandali yayinda ta fito farfajiyar gada za ta bada waka. Akan ji yarinya ta na koda nau'in sanai'ar gidan su mijin ta da fidda a matsayin na karfen nata. Da ga nan kuma sai magabata su Ankara su shigo maganar. Akwai misalan irin wannan na da dama a cikin wasu wakokin dandali da adabin baka ya adana ma na su har mu ka san su a yau. Amma da zamani ya nisa kuma bakin al'adu da ilimin yamma ya shigo ma na sai abubuwan su ka sauya. Gadar ma yanzu wata ba ta san yadda ake yi ba. A halin yanzu dai yan mata na ganin cewa wata mummunar faduwa ce ko zubar sa aji ace wai mace ta nemi soyayyar saurayi. Wannan girman kan da zurfin cikin ko Kuma na ce nauyin bakin ya dade ya na sanya yan mata su na bugewa da auren mijin da ba sa ka...