Maraba Lale

Barka da shigowa wannan farfajiya ta yanar gizo da zata dinga kawo mu ku zafafan bayanai kan duk abubuwan da su ka shafi zamantakewar miji da mata a gidajensu na aure. Za mu dage ƙwarai wajen gudanar da bincike mai zurfi kan matsaloli da nufin nemo bakin zaren don ganin sunnan Ma'aiki bata samu tazgaro ba.
Za mu mai da hankali kan ba da shawarwari da misalai kan matsolin wasu ma'auratan domin waɗanda ba su da irin waɗannan matsalolin su shafawa na su gemun ruwa.
Wajen da ya kamata a fayyace wani abu kuma, to fa za mu cire kunya mu yi bayani dalla-dalla cikin sanin yakata da kuma riƙo da al'adun mu kyawawa da addinin mu ba tare da an mayar da shafin kamar wani shafin yaɗa batsa da motsa sha'awar matasa ba.
Hakazalika akwai lokutan da zamu dinga kawo magungunan wasu daga cikin manya manyan cutukan da ke tarwatsa zamantakewar aure da kuma nuni da inda za'a sami waɗannan magungunan domin mutun ya haɗa da kansa ko kuma inda zai yi ya mallaki haɗaɗɗe cikin sauƙi da ikon Allah SWT.
Allah kaɗai ne zai taimaka mana wajen idda nufin wannan aikin ƙwarai da mu ka ɗauki gabarar aiwatarwa domin ceto rayukan aure da dama da ga macewa ko kuma samun mutuwar ɓarin jiki.
Mu na fatan za'a fahimce mu sarai da kuma manufofin mu a wannan gagarumin aikin da ya ke kama da ɗaukar Dala ba gammo. Amma tunda mun riga mun nemi taimakon Allah Maɗaukaki ba wata irinmatsala kuma duk girmanta da za ta iya sha mana gaba.

Comments

Popular posts from this blog

HUTSUN MIJI DA MACE MAI TSIWA

GIDAN AURE MAI CIKE DA HATSANIYA

MATSALAR SHAYE-SHAYE