MATSALAR TATTALIN ARZIƘI
MATSALOLIN DA SU KA ADDABI RAYUWAR AURE (cont.) 8) MATSALAR TATTALIN ARZIKI Allah shi ne cikakken Mawadaci kuma Abin Godewa. Duk sauran mutane kuwa masu buƙatuwa ne zuwa gare Shi. Wasu lokutan aure kan zo da camfi ko afkuwar matsalar ƙuncin rayuwa sanadiyyar nauyaye-nauyayen da su kan hau kan magidanta da kuma rashin samun ƙarin wasu hanyoyin damun kuɗaɗen shiga sannan da rashin tsarin kasafin kasashe kuɗaɗe da mu ke yi a yawancin lokuta. Wa su su fara canfa amarya da cewa mai farar ƙafa ce da makamantan waɗannan zantukn. Wannan na zama babbar barazana idan aka sami rashin fahimtar yanayin rayuwar musamman da ga ɓangaren mata. Sau da yawa matsalar matsin tattalin arziƙi da ƙuncin rayuwa ta janyo macewar aure bida adadin. Wani magidancin ma idan garin ya yi masa zafi arcewa ya ke ya bar iyayen yarinya da ɗaukar nauyinta, idan abin ya tsananta kuma alƙali ya bata gaiba a kashe auren ɗungurungun. Shwara ga matan...