Posts

Showing posts from September, 2021

MATSALOLIN DA KE ADDABAR AURE A KASAR HAUSA

Mata kan ce wai aure raine da shi. Amma alamu na nuna cewa tsahon ran auren iyayen mu da kakanninmu ya fi na mu tsaho nesa ba kusa ba. Tunda ana samun auren da ya zarta shekara sittin a da, amma yanzu har auren kwana uku an samu a kasar Hausa. Wannan babban dalilin da ya sa wasu kabilun da su ke kallon Bahaushe da ga nesa su ke hana su auren yayansu. A kasa mun sake kawo wasu jerin dalilan da su kan kawo mutuwar aure cikin kankanin lokaci kamar yanda muka taba kawowa a wani rubutu da muka walƙafa a baya. 1) Rashin tsoron Allah 2) Rashin daukar aure a matsayin ibada 3) Karya kafin aure 4) Matsalar jahiltar auren ma kansa 5) Matsalolin rashin gyaran turaka 6) Matsalar rashin iya girki 7) Matsalar shaye-shaye 8) Matsalar tattalin arziki 10) Matsalar surukai (iyayen ma'aurata) 11) Matsalar abokiyar zama 12) Matsalar facala 13) Matsalar dangin miji ko mata 14) Matsalar zaman gidan haya 15) Matsalar makota 16) Matsalar miyagun abokai da kawaye 17) Matsalar cutuka 18) Ma...

Maraba Lale

Barka da shigowa wannan farfajiya ta yanar gizo da zata dinga kawo mu ku zafafan bayanai kan duk abubuwan da su ka shafi zamantakewar miji da mata a gidajensu na aure. Za mu dage ƙwarai wajen gudanar da bincike mai zurfi kan matsaloli da nufin nemo bakin zaren don ganin sunnan Ma'aiki bata samu tazgaro ba. Za mu mai da hankali kan ba da shawarwari da misalai kan matsolin wasu ma'auratan domin waɗanda ba su da irin waɗannan matsalolin su shafawa na su gemun ruwa. Wajen da ya kamata a fayyace wani abu kuma, to fa za mu cire kunya mu yi bayani dalla-dalla cikin sanin yakata da kuma riƙo da al'adun mu kyawawa da addinin mu ba tare da an mayar da shafin kamar wani shafin yaɗa batsa da motsa sha'awar matasa ba. Hakazalika akwai lokutan da zamu dinga kawo magungunan wasu daga cikin manya manyan cutukan da ke tarwatsa zamantakewar aure da kuma nuni da inda za'a sami waɗannan magungunan domin mutun ya haɗa da kansa ko kuma inda zai yi ya mallaki haɗa...